Toshon gwamnan jihar Zamfara Sanata Ahmad Sani Yariman Bakura ya yaba da matakan cire tallafin man fetur da na daidaita farashin dala da shugaban Najeriya Bola Tinubu ya É—auka.
A wata tattaunawa da BBC Yariman Bakura ya ce shugaban ƙasar ya ɗauki matakan da wasu shugabanni ƙasar suka kasa ɗauka.
Ya ƙara da cewa matakan biyu an daɗe ana shan alwashin ɗaukarsu, amma ba a cika ba sai a yanzu.
''Waɗannan matakan ko Buhari da ya gabata ya sha cin alwashin ɗaukarsu, amma ƙarshenta sai ya ɗaga zuwa watan shida, bayan kuwa ya san a watan biyar zai ƙare mulki'', in ji tsohon ɗan majalisar dattawan.
Yariman Bakura ya ce, duk da cewa za a samu tsanani a farkon waÉ—annan matakai, amma akwai fatan samun sauki nan gaba.
''Kamar yadda kowanne musulmi ya san cewa Allah (S.W.T) ya ce a cikin kowanne tsanani a kwai sauƙi, dama sai an ɗauki matakai da mutane daga farko suke ganin kamar an tsananta musu'', in ji shi.
BBC