Shugaban Najeriya Bora Ahemd Tinubu ya amince ca kafa asusun gina ababen more rayuwa a jihohin kasar 36, a wani mataki na rage wa yan kasar radadin cire tarafın man fetur.
Shugaban ya amince da matakin ne a lokacin taron wata wata na kamitin kula da asusun raba kudin, shiga na gwamnatin kasar (FAAC) da aka gudanar ranar Alhamis a Abuja.
Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar Dele Alake ya fitar, ya ce sabon asusun zai taimaka wa jihohin kasar wajen zuba jari a bangarorin sufuri da harkokin noma da gina tituna da kasuwanni da kiwon dabbobi da bangaren lafiya da ilimi musamman a matakin farko, da wutar lantarki da ruwan sha domin habaka tattalin arzki da samar da ayyukan yi ga yan kasar.
Kwamitin ya kuma amince da ajiye wani bangare na kudin da ake rabawa a kowane wata domin takaita tasirin aeruwar shiga da za a iya samu sakamakon matakan cire tallatin mai da daidata farashin dala tare da hauhawar farashin kayayyaki za su iya haifarwa.
Kwamitin ya ce daga cikin naira tiliyan 1.9 na kudin shigar da aka samu a watan Yunin 2023, naira biliyan 907 ne kawai za a raba tsakanin matakan gwamnatin kasar uku, yayin da za a ajiye naira biyan 790 a asusun.
Wadannan kudaden da za a riƙa ajiyewa za su taimaka wajen samar da asusun gina ababen more rayuwa tare da aiwatar da wasu abubuwa, domin tabbatar da an yi amfani da kudin tallafin wajen gina muhimman abubuwan ci gaba, domin inganta rayuwar yan kasar kamar yadda sanarwar ta bayyana.
Haka kuma kwamitin ya yaba wa shugaban kasar bisa matakin cire tatafin man tare da bullo da matakai daban-daban na tallafa wa 'yan kasar domin rage masu raÉ—adin cire tallafin