Sun ce yin kitso ga maza daɓi'a ce da ta saɓa wa doka da al'adun gargajiya kuma barazana ce ga tarbiyyar mutane.
Sakataren raya al'adun yankin na Zanzibar Omar Adam ya ce kitson da wasu maza suke yi , wata al'ada ce da aka ɗauko daga wajen yankin.
Omar Adam ya yi watsi da damuwar da wasu suka nuna a kan cewa matakin zai shafi yan luwadi da maɗigo da ke zaune a tsibirin inda aka haramta auren jinsi ɗaya..
Sai dai duk da cewa dokar da ta hana maza yin kitso ba sabon abu ba ne, saboda tun shekarar 2015 ne aka zartar da ita amma a yanzu ne mahukuntan Zanzibar suka aiwatar da ita.
Dokar dai ta yi tanadin cewa duk wani namiji da ya shiga yankin da kitso ko yana zaune a cikin yankin, za a ci tarar fiye da dala 400, ko kuma ɗaurin wata shida a gidan yari ko hukuncin duka biyun.
Sai dai duk da cewa Zanzabir na cikin wuraren da masu yawon buɗe ido suke son zuwa amma mahukunta yanki sun ce dokar za ta yi aiki kan baki.
A cikin watanni biyu da suka gabata ne gwamnatin Zanzibar ta haramta wasu sunayen littattafai 16 da kuma amfani da launukan bakan gizo a makarantu saboda a cewarsu suna goyon bayan masu kare hakkin 'yan luwadi da maɗigo