Majalisar ta amince da dokar ce don noma nau'in wiwin da za a iya amfani da shi a masana'antu da kuma na magani.
Dokar hukumar yaki da miyagun kwayoyi da aka yi wa gyaran fuska za ta bai wa ma'aikatar harkokin cikin gida damar bai wa masu son noman ganyen wiwi lasisi.
A bayan kotun daukaka karar kasar ta soke gyare gyaren dokar wadanda suka halasta noman wiwi domin samar da magani.
An hana noman ganyen wiwi a kasar ta Ghana ne saboda damuwar da ake da ita a kan matasa na shanta.
Yanzu dai dokar na bukatar sanya hannun shugaban kasar Nana Akufo Addo don fara aiwatar da ita.