Laifin mutumin ya haɗa da sayarwa da safarar ƙwayar sanadarin methamphetamine mai ɗimbin yawa.
Rahotanni sun ce an zartar da hukuncin ne a arewa maso yammacin ƙasar.
Iran na yawan zartar da hukuncin kisa a kan laifukan da suka jiɓanci safarar ƙwaya, sai dai ƙungiyoyin kare hakkin bil'adama na nuna damuwa kan yawaitar zartar da hukuncin kisa a ƙasar.
Inda ake zargin cewa gidajen yarin ƙasar sun zamo wasu cibiyoyin zartar da hukuncin kisa.
A farkon wannan wata ne wata ƙungiyar kare hakkin bil'adama da ke zama a birnin Oslo ta ce kimanin mutum 400 ne aka zartar wa hukuncin kisa a ƙasar cikin wata shidda da suka wuce.