Yayin da rahotanni ke cewa an dan samu natsuwa a yanzu, bayan rikicin kabilancin da aka shafe kwanaki ana yi a jihar Taraba, bayanai na cewa mutane da dama musamman wadanda suka tsere wa gidajensu ko aka kona musu sun shiga mawuyacin hali.
Rikicin ya faru ne tsakanin 'yan kabikar Karimjo da Wurkun, sanadiyar sarauta.
Hon Abdullahi Mohammed dan majalisar dattawa da ke wakiltar yankin ya shade wa BBC cewa cikin kwana biyun nan rikicin ya dan lafa, sakamakon matakan da gwamnati da jami'an tsaro suka dauka, amma mutane na cikin tashin hankali.
Ya ce ''Ana cikin mawuyacin hali, musamman wadanda aka konawa gidajensu, mata da yara sun bar gidajensu, ga shi kuma damina ce lamarin ya munana, babu inda za su je su zauna''
Ya kara da cewa yawancinsu da suka gudu sna zaune ne a makarantu, yayin da wasu kuma ke tare da 'yan uwansu da dama can suma suna ji da kansu.
Hon Abdullahi Muhammad, ya ce akwai bukatar kai agajin gaggawa ga irin wadanan mutane da wuri, musamman na abinci da kayan sawa da kuma mayafai.