Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta bayyana sunayen wasu Matasa da su gaggauta kai kansu Shalkwatar rundunar, ko kuma ta sanya kafar wando daya da su.
Matasan sun hada da:
1. Burakita Dorayi
2. Messi Kantudu
3. Danbos Dala
4. Ado Runtu Bachirawa
5. Baffa Killer M/Tanko
6. Kamilu Duna Adakawa
7. Cile Maidoki T/Fulani
8. Huzaifa Yola
9. Hantar Daba K/Diso
10. Nasir Nasiru Zango
11. Nazifi Nanaso Zango
12. Sharu Ali Sharifai
13. Ma'aruf Goma
14. Bahago K/Bulukiya
15. Zubairu Mai dala
16. Sharu Gambo
Kwamishinan yan sandan jihar CP Muhammad Usaini Gumel, ne ya bayyana sunayen yayin da yake holin wadanda ake zargi da aikata laifuka su kimanin 108.
Abdullahi Haruna Kiyawa
6/7/2023