An samu bullar cutar mashako a wasu sassan jihar Osun, wadda ta yi sanadin mutuwar wani yaro dan shekara shida.
Gwamnan jihar, Ademola Adeleke, ya bayar da umarnin a sake farfado da cibiyar bayar da agajin gaggawa kan harkokin lafiya ta jihar nan take.
Sannan ya bada umarnin a kara kulawa da wadanda suka kamu da cutar da aka gano.
Tuni dai gwamnatin ta fara tuntubar cibiyar kula da cutuka ta kasa don musayar bayanai da dakile barkewar duk wata cuta.
Ma'aikatar lafiya a jihar ta Osun ta ce nan ba da jimawa ba za ta dauki matakai na yi wa yara allurar rigafi.
Ma'aikatar ta kuma shawarci iyaye da su tabbatar an yi wa yaransu rigafin idan aka fara tare da gujewa wuraren cunkoson jama'a