Matsalar barace-barace da yaran da suka isa zuwa makaranta ke yi ba sabon abu ba ce a yankin sai dai galibi maza ne ke yi.
Game da wannan matsala hukumomi a Hadejia da ke jihar Jigawa suka dauki matakin hana barace-baracen, bayan da aka samu wasu mata mabarata an yi musu ciki tare da mayar da su garuruwan su na asali.
Bayanan da BBC ta samu na cewa mabaratan maza da mata suna kwarara ne cikin garin Hadejia daga ciki da wajen jihar Jigawa, don yin bara inda suke bi tashoshin mota da kasuwanni.
A baya-baya matsalar ta yi kamari inda mazauna yankin suka ce al'amarin ya kai ga ana cin zarafin wasu daga cikinsu.
Game da wannan matsala dai karamar hukumar Hadejia ta samar da wani kwamiti wanda ya bincika batun sannan ya bayar da shawararin abin da ya kamata a yi.
Akasarin matan da aka kama din ba su da takamaiman wurin kwana sai dai watangaririya da suke yi.
Mahukunta a Hadejan sun ce yaran da suke gararamba ‘yan asalin karamar hukumar Hadejan musamman marasa galihu, za a yi musu tsari don tsugunar da su tare da sanya su a makaranta.