Farashin man fetur ya karye a defo-defo na Najeriya a daidai lokacin da ake raɗe-raɗin ƙarin farashin man zuwa naira 700 a kan duk lita ɗaya cikin wannan wata na Yuli.
Ƙungiyar dillalan man fetur ta Najeriya, IPMAN ta tabbatar da karyewar farashin, ta ce ana sayar da shi a kan naira ɗari huɗu 400 da ɗoriya, saɓanin sama da naira ɗari biyar a kan duk lita ɗaya.
Shugaban ƙungiyar reshen arewacin Najeriya, Bashir Ahmed Danmalam ya shaida wa BBC cewa farashin ya karye ne saboda ƙarancin masu saye, kuma za a samu rangwamen har a gidajen mai.