Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa a baya-bayan nan ne babbar kotun Majistaren jihar ta umarci tsare shi a hannun hukumar karɓar ƙorafe- ƙorafe hana cin hanci ta jihar Kano (KPCACC).
An zargi tsohon kwamishinan da yaudara da kuma yin karya a takardun wasu ayyuka zamanin gwamnatin da ta wuce.
Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta Kano ta yi zargin cewa a 2023, tsohon kwamishinan ya bai wa kamfanin Arafat construction da 'Multi resources' kudi nairan biliyan ɗaya domin gyaran tituna 30 a cikin birnin jihar.
To sai dai in ji hukumar, babu ko É—aya cikin ayyukan da aka yi. A baya-bayan nan dai hukumar KPCACC ta ce ta aike da takardar gayyata ga tsohon gwamnan jihar Abdullahi Ganduje a kan 'bidiyon dala'.
To amma babbar kotun tarayya a jihar ta dakatar da hukumar a kan wannan batu, har zuwa lokacin da za ta kammala sauraron ƙorafin da Ganduje ya shigar gabanta yana neman ta hana hukumar binciken sa.