Ƙasashen Indiya, Najeriya da Pakistan ne ke da mafi yawan mutane masu fama da irin wadannan cututtukan, a cewar wani sabon bincike da aka buga a mujallar Lancet.
An gano cewa cututtuka masu yaduwa sun haddasa fiye da rabin irin wadannan mace-mace a kasashe masu karami zuwa matsakacin karfi, idan aka kwatanta da kashi 6 cikin 100 na kasashe masu karfin tattalin arziki, binciken da Cibiyar Nazarin Yara ta Murdoch da ke Australia, da Cibiyar kididdigar alkaluman kiwon lafiya ta Amurka ta ce.
Binciken da aka yi a cikin kasashe 204 daga tsakanin shekarun 1990 zuwa 2019, ga mutane daga lokacin haihuwa zuwa shekaru 24, ya gano matakan hana kamuwa da cuta sun fi mayar da hankali kan yara 'yan kasa da shekaru biyar, tare da karancin kulawa ga matasa tsakanin shekaru biyar zuwa 24.
Bayan la'akari da wadannan sauye-sauyen alƙaluman nauyin cututtukan, binciken ya yi kira da duk yunkurin da ake yi na magance cututtuka a duniya su mayar da hankali kan yaran da suka tasa da kuma matasa.
Cututtuka kamar gudawa, da ciwon huhu da zazzabin cizon sauro sun kai kashi biyu bisa uku na cututtuka masu yaduwa da ke haddasa mutuwa a cikin wannan adadi, yayin da cuta mai kashe garkuwan jiki da tarin fuka aka gano su ne kan gaba cikin cututtukan da ke addaban matasa.
BBC