Wannnan na zuwa ne ya yin da hukumar ta ce ta lura wasu 'yan kasuwar na zuba shara a wuraren da ba su kamata ba, al'amarin da yasa sharar ke taruwa ta cunkushe hanyoyi.
REMASAB ta sanar da cewa nan gaba kadan za a É“ullo da wani shiri da zai tilasta wa masu shaguna da motocin haya saka kwandon shara a cikin mota da wuraren kasuwanci.
Shugaban hukumar Alhaji Ahmadu Haruna Zago, ya shaida wa BBC cewa, bayanan da suka samu akwai wuraren kasuwanci da dama a sassan jihar, da ake zuba shara-barka-tai, al’amarin da yace ba za su lamunta ba.
Ahmadu Zago, ya ce za su kalli dokokin hukumar kwashe shara da dokokin jiha da na kasa wadanda suka yi tanade-tanade game da irin wadannan matsaloli wajen yin hukunci.
Jihar Kano wadda ke kan gaba wajen yawan al’umma a arewacin Najeriya, na fama da matsalar shara, inda a wasu unguwanni wari da hayaki ke addabar jama’a da kuma barazanar ambaliya saboda cushewar magudanan ruwa.