Ana ci gaba da yi wa wani matashi tambayoyi wanda aka kama bisa zargin yunkurin kisan bayan harin da ya kai a Tewkesbury Academy, in ji 'yan sandan Gloucestershire.
An kai malamar asibiti da rauni a ranar Litinin amma daga baya aka sallame ta.
‘Yan sanda sun ce za su rika kai samame a yankin nan da kwanaki masu zuwa domin kwantar da hankulan mazauna yankin.
A lokacin da abin ya faru, an gaya wa wasu makarantu biyu na yankin da su rufe yayin da ‘yan sanda ke farautar wanda ake zargin da caka wa malamar makarantar wuƙa.
Shi dai matashin da ake zargi an kama shi ne bayan sa'o'i biyu a ƙauyen Stoke Orchard mai nisan mil huɗu, bayan farautarsa da jami'ai suka yi.