Gwamnatin Najeriya ta ce za ta rage shigaR da magunguna cikin ƙasar daga kashi 60 zuwa kashi 40 kawai cikin 100 domin bunkasa harkar sarrafa magunguna a cikin gida.
Mai bai wa shugaban kasa shawara ta musamman kan harkar lafiya, Salma Anas-Ibrahim ce ta bayyana hakan a wani taron ƙarawa juna sani da aka shirya domin karfafa dabarun hadin gwiwa tsakanin Hukumar Lafiya ta Duniya a Abuja.
A cewarta, wannan wani ɓangare ne na burin da Shugaba Bola Tinubu ya sanya gaba da nufin cike giɓin da ake samu a fannin kula da lafiya na ƙasar.
Sauran fannonin da sabuwar gwamnatin za ta fi bai wa fifiko sun haɗar da haɓaka damar samun ayyukan kula da lafiya ga kowa da kowa da shigar da al'umma cikin shirin inshorar lafiya na ƙasa da aƙalla kashi 40% don tabbatar da ganin duk 'yan Najeriya ciki har da rukunin al'umma masu ƙaramin ƙarfi.