Hukumomin sun É—auki matakin ne domin kauce wa hadarin da ke tattare da tsananin zafin da za a yi fama da shi a goben.
A nata bangaren, hukumar Alhazai ta Najeriya, NAHCON ta jaddada wa mahajjatan Najeriya da su dauki matakan guje wa tsananin zafin ranar da za a fuskanta ta hanyar bin shawarar hukumomin na Saudiyya na yin sallar juma’a a masallatan da ke kusa da inda suke zama.
Daraktan ayyukan gudanarwa da al’amuran ma’aikata na hukumar, Dokta Ibrahim Sodangi ya shaida wa BBC cewa bijire ma wannan shawarar na iya sanya mahajjata a wani mawuyacin hali ta hanyar haifar da kalubale ga lafiyar jikinsu.
Daraktan ya bayyana cewa an shafe shekaru da dama ba a sami yanayi mai irin wannan tsananin zafin ba don haka ya ƙara yi kira ga mahajatan Najeriya su yi ƙokarin guje wa shiga rana ba tare da ƙwaƙƙwaran dalili ba.