Shugaban hukumar kwashe shara ta jihar Kano Ambassador Alhaji Ahmadu Haruna Zago yace nan gaba kadan gwamnati zata Samar da tsarin da zai Kara jaddada dokar Hana zubar da shara barkatai musamman a wuraren da idan gwamnati ta kwashe al'umma suke sake zubawa.
Shugaban ya bayyana hakan ne lokacin da yake tattaunawa da manema labarai a zagayen gani da ido da yake yi kan yadda aikin kwashe shara ke cigaba da gudana a wasu sassan jihar Kano.
Yace duba da yadda wasu daga cikin al'ummomin da aka kwashe sharar su a kwanakin baya suka sake jibge sharar a wuraren,
hakan na nufin dole sai gwamnati ta fito da tsarin da zai karfafa dokar zubar da shara ga al'umma musamman a wuraren da aka tana da domin zubarwa.
Suma wasu daga cikin al'ummomin da aka kwashe sharar dake yankunansu musamman na kan titin Katsina da makabartar abbatuwa sun bayyana irin cikakken hadin kan da zasu bawa gwamnati domin tsaftace Muhallansu da titunan.