Sabon kwamandan hukumar Hisbah na jihar Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya ce zasu ɗaura auren 'yan mata da zawarawa 1,000 a faɗin jihar Kano, inda za su rarraba fama-famai guda 20 ga kowace ƙaramar hukuma daga cikin ƙananan hukumomi 44 dake Kano.
Daurawa ya bayyana haka ne cikin jawabinsa na ranar farko da ya shiga Ofis bayan gwamnan Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf (Abba Gida Gida) ya sake naÉ—a shi a matsayin babban kwamandan hukumar ta Hisbah, wacce ke umarni bisa aikata kyakykyawan aiki, tare da hani ga aikata mummunan aiki.
Tun a lokacin yaƙin neman zaɓe, Abba ya sha alwashin aurar da zawarawa kamar yadda aka yi a lokacin mulkin tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.