Gwamnan ya dauki matakin ne da nufin kare irin wadannan masu sana'a da ci gaba da kashensu da 'yan Boko Haram ke yi a wajen garuruwan kananan hukumomin jihar.
Ba a san adadin matasan da ke irin wannan sana'a da ke tafiye tafiye zuwa garuruwa don sana'arsu da aka kashe ba.
Da yake sanar da matakin, gwamna Zullum, ya ce," A cikin shekaru biyar da suka wuce, an kashe mutane da dama a sakamakon yawan jari bola da suke abin da ya janyo gwamnatin jihar ta fara bincike a kai ke nan."
Ya kara da cewa, " Kuna ganin wannan wajen, duk waje ne mallakin gwamnati, sannan daga baya kuma waje ne mallakin kamfanonin sadarwa. A don haka irin wadannan sana'oi zagon kasa ne da ake yi wa gwamnatin tarayya, a don haka na bayar da umarnin dakatar da wannan sana'a."
Zullum, ya ce yawancin masu irin wannan sana'a kuma na lalata kayayyakin gwamnati da ma na kamfanoni masu zaman kansu a don haka ba za a amince da irin wadannan mutane ba.
Gwamnatin jihar ta ce zata yi aiki kafada da kafada da hukumomin tsaro don tabbatar da an kama duk wanda ya nuna kunnen kashi ko ya karya doka.