Gwamnan ya bayyana É“acin ransa a lokacin da ya kai wa asibitin ziyarar ba-zata da tsakar daren ranar Asabar.Cikin wata sanarwa da gwamnan ya wallafa shafinsa na Twitter, ya ce ya kwana a garin wanda shi ne shalkwatar karamar hukumar Gwoza da ke kudancin jihar.
A ziyarar Zulum ya kewaya sassan asibitin domin duba irin kayayyaki da yadda asibitin ke aiki.
A lokacin ziyarar gwamnan ya nuna damuwarsa kan yadda ya samu asibitin.
Ya ce ''Abin takaici ne halin da babban asibitin garin Gwoza ke ciki, babu manyan abubuwan buƙata a asibitin kamar wutar lantarki. Hakiƙa hakan zai kawo cikas da cutarwa ga marasa lafiyar da ke kwance a asibitin, tare da durƙusar da shirinmu na inganta asibitoncin jiharmu''.
Gwamnan ya kuma nuna ɓacin ransa kan rashin sanar da shi halin da asibitin ke ciki.''Ba zan iya wanke kai na ko ƙaramar hukuma daga wannan laifi ba, dukanmu mun gaza samar da abin da ake buƙata''.
Zulum ya kuma tabbatar wa da marasa lafiyar da ke kwance a asibitin cewa za a magance matsalolin da asibitin ke fuskanta, inda nan take ya bayar da umarnin fara gyara wuraren da suka lalace ciki har da wutar lantarkin asibitin.
Haka kuma gwamnan ya yaba wa ma'aikatan asibitin, waɗanda duk da rashin hali mai kyau da asibitin ke ciki ya same su a bakin aikisu, inda ya alƙawarta saka mu da alkairi kan sadaukarwar da ya ce suna yi duk kuwa da tarin kalubalen da suke fuskanta.
Gwamna Zulum ya saba kai irin wannan ziyara ta ba-zata zuwa makarantu a asibitoci a fadin jihar, a wani yunƙurin na sanin haƙiƙanin halin da suke ciki.