"Yana Da Kyau Mu San Dalilin Yin Wannan Appeal Din. An Yi Wannan Appeal Ne Bisa Shigo Da Shedar Dr. Aminu Idris Harbau Ba Bisa Ka’ida Ba, Musamman Lokacin Da Ya Kamata A Shigo Da Shedar Ta Sa Ya Wuce Kuma Ba Su Nemi A Tsawaita Musu Lokaci Ba, A Sakwamakon Haka Ne His Excellency Engr. AKY Ta Hannun Babban Lauyan Sa Chief Adegboyega Awomolo, SAN Ya Yi Appeal.
An Tafi Appeal Ne Tun Kafin Wannan Shaida Ya Zo Ya Bada Shaida Kuma Bayan Ya Bada Shaidar Aka Ga Tafiya Appeal Din Ma Ba Shi Da Wani Amfani Ta Yadda Aka Yi Watsa Watsa Da Shaidar Shi Dr. Aminu Harbau Din A Wurin Cross Examination Ma'ana Lokacin Da Lauyan His Excellency Engineer AKY Chief Adegboyega Awomolo, SAN Yake Masa Tambayoyi Inda Ya Masa Tambayoyi Kamar Haka Kuma Ya Bada Amsoshi Kamar Yadda Suke A Cikin Tambayoyin:
1. A Sakin Layi Na Bakwai Na Shaidar Ka Ka Ce All People's Congress Ne Suka Ba Ka Aiki Yace A'a All Progressive Congress Ne Bayan Kuma A Rubuce All People's Congress Ne.
2. Ya Tambaye Shi Duk Wani Analysis Ba Zai Cika Ba Sai An Yi Shi Daidai Kuma Babu San Zuciya Yace Eh Sai Yace Masa Tebur Din Ka Na Daya Da Na Biyu Total Din Ba Daidai Ba Ne Yace A'a Daidai Ne Sai Ya Ba Shi Kalkuleta Yace Ka Buga Lissafin Ka Gani Ya Buga Ya Kasa Fadar Amsa Sai Lauyan Yace Masa Kada Ka Bata Mana Lokaci Ka Yarda Lissafin Ba Daidai Ba Ne Yace Eh Ba Daidai Ba Ne To Kuma Wane Shiririta Za Ku Zo Kuna Yi Bayan An Yi Discrediting Din Shaidar Na Ku Wanda Ranar Da Aka Fito Sai Da Suka Ji Kamar Su Yi Masa Dukan Tsiya.
3. Ya Kuma Tambaye Shi Kai Ma'aikacin Gwamnati Ne Yace Eh Sai Yace Da Izinin Wanda Suka Dauke Ka Aiki Ka Zo Bada Shaida Yace A'a
4. An Tambaye Shi Wannan Lissafin Da Ka Yi Babu Wani Abu Special A Ciki Tunda Ko Sun Alkalan Nan Guda Uku Aka Bawa Aikin Warewa Da Lissafawa Za Su Iya Yace Eh".
~~Barr. Barr Badamasi Suleiman