Kungiyar kare hakkin bil'adama ta Human Rights Watch ta ce, kotun hukunta manyan laifuka ta kasar Saudiyya da aka fi sani da kotun yaki da ta'addanci ta yanke hukuncin kisa ga dan kasar Mohammed Al-Ghamdi sanadiyyar wasu abubuwan da ya wallafa a shafinsa na X da kuma ayyukansa a shafin YouTube, inda aka yi amfani da abubuwan da ya wallafa a matsayin shaida a kansa.
Al-Ghamdi, wanda malami ne wanda ya yi ritaya kuma dan shekara 54, an yanke masa hukuncin kisan ne a ranar 10 ga watan Yuli.
Takardun kotun da Human Rights Watch ta duba sun nuna cewa dalilin da ya sa aka yanke masa hukuncin kisa shi ne bisa kama shi da laifukan da suka shafi sarki ƙasar da kuma yarima mai jiran gado, kuma laifukan sun tsananta ne saboda kasancewar su a dandalin watsa labarai na duniya wanda ke bukatar hukunci mai tsanani.
Joy Xia, mai bincike kan al'amuran Saudiyya a kungiyar kare hakkin bil'adama ta Human Rights Watch, ta bayyana damuwa kan abin da ta bayyana a matsayin wani sabon mataki mai ban tsoro a Saudiyya inda kotu za ta iya zartar da hukuncin kisa kawai saboda wallafa sako a dandanlin sada zumunta.
Kawo yanzu dai babu wani martani daga gwamnatin Saudiyya dangane da wannan batu.