Mutanen da aka maye gurbin kujerun nasu sun haɗar da mataimakin shugaban jam'iyyar na kasa, shiyyar arewacin Sanata Abubakar Kyari, wanda aka naɗa muƙamin ministan harkokin noma da samar da abinci.
Inda aka naÉ—a shugaban jam'iyyar na jihar Borno Ali Dalori a matsayin wanda zai maye gurbinsa.
Sai kuma Mary Alile Idele da ta maye gurbin Dakta Betta Edu a matsayin shugabar mata ta jam'iyyar
Shugaba Bola Tinubu ya naɗa Dakta Betta Edu a matsayin ministar harkokin jin-ƙai da kawar da talauci.