Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya karyata rade-radin da ake yadawa na kwace filin ajiye motoci na Rijiyar Zaki.
Cikin Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, ta ce, labarin da ake yadawa wani barna ne da ake kokarin kawo wa gwamnatin da ba ta dace ba don dauke hankalinta daga dimbin nasarorin da aka samu zuwa yanzu.
Sai dai sanarwar ta yi kira ga jama’a da su yi watsi da duk wani bayani da ya shafi raba wa wani mutum ko kungiya wani fili na jama’a domin gwamnati ta kuduri aniyar kare wuraren taruwar jama’a domin amfanin al’ummarta da mazauna jihar.