Ministan kuɗi da harkokin tattalin arziƙi, Cif Wale Edun ne ya bayyana haka a ƙarshen taron Majalisar Zartarwar Ƙasar na farko ranar Litinin a Abuja.
Ya ce amfanin da aka samu daga cire tallafin man fetur, za a zuba shi a ɓangarori daban-daban da za su taimaka wajen bunƙasa kuɗaɗen shiga ga gwamnati da inganta kasuwanci a cikin gida da kuma samun zuba jari daga ƙetare.
Wale Edun ya ce bayan ƙarin kuɗin shigar da aka samu sakamakon cire tallafin man fetur, an tsara matakan fitar da tallafin rage raɗaɗi na taƙaitaccen wa'adi da matsakaici da kuma dogon lokacin.
Ya jaddada cewa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu na muradin farfaɗo da tattalin arziƙin Najeriya daga mawuyacin halin da yake ciki nan da wani ɗan lokaci.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN ya kuma ruwaito ministar masana'antu da kasuwanci da harkokin zuba jari, Doris Uzoka-Anite na cewa tuni har an fara samun masu tayin zuwa Najeriya don zuba jari a fannoni daban-daban na tattalin arziƙin ƙasar ciki har da ɓangaren man fetur da iskar gas da lafiya da haƙar ma'adanbai da kuma noma.