Wannan batu ya soma ɗaukar hankali ne tun lokacin da wasu kafofin yada labarai na Najeriya suka kwarmata cewa Hannatu Musawa ta karbi muƙaminin minista ba tare da kammala aikin hidimar kasa ba.
Da fari labarin ya soma kamar jita-jita, sai dai sannu a hankali sai hankula suka fara karkata kan batun, aka kuma riƙa samun ƙarin kafafe da ke fito da batun da kuma zargin cewa ta karya dokar ƙasa.
Sai dai daga baya an ga wata sanarwa da galibin kafofin yaɗa labarai suka wallafa inda a ciki ministar ke cewa ba ta karya kowacce doka ba, bayan karɓar mukaminta na minista.
Sanarwar da aka fitar dauke da kwanan watan 27 ga watan Agustan 2023, ya kasance abin da ya riƙa yawo a jaridu da kafofin watsa labarai har da sociyal midiya a ƙarshen mako.
Amma daga bisani ma'aikartar yada labaran Najeriya ta fitar da bayanin cewa wannan sanarwa ba daga wurin Ministar ta fito ba.
To ko me ya sa wannan batu na bautar kasar Hannatu Musawa ya dauki hankali, sannan me 'yan Najeriya ke cewa, kuma me doka ta tanada kan wannan batu?
Dambarwar NYSC da Hannatu
Mako ɗaya ke nan bayan rantsar da ministoci, kuma tun daga wannan lokaci ake ta ce-ce-ku-ce kan batun sabuwar ministar Hannatu Musawa, bayan gaza gabatar da takardar kammala shirin NYSC.
Batun ya sake daukar sabon fasali bayan hukumar NYSC ta tabbatar da cewa yanzu haka Hannatu mai shekara 49 tana gudanar da hidimar ƙasa, abin da ya tunzura mutane da sake buɗe kafa ta muhawara mai ƙarfi.
Sai dai Hannatu Musawa da aka tabbatar yanzu haka na cikin wata na takwas daga cikin shekara guda na shirin hidimar ƙasa, bayanai na nuna cewa an shafe tsawon lokaci ana tababa kan batun bautar ƙasar tata.
Wasu bayanai da BBC ta tattara sun nuna cewa a shekara ta 2001 ministar ta fara rajistar yin hidimar ƙasa, inda aka tura ta jihar Ebonyi, wanda bayan wani zama na gajeren lokaci ta nemi sauyin wuri ta koma Kaduna. Sai dai babu tabbas ko ta kammala hidimar ba a wancan lokacin.
Sannan akwai wasu bayanai na daban kuma da ke cewa a 2003 ta kammala bautar kasarta amma sai aka riƙe mata takardar shaidar kammalawa, yayin da NYSC ke cewa ta ajiye hidimar kasar ne ba tare da ta kammala ba, lamarin da ya sa aka riƙe takardar tata.
Bayan tsawon shekaru na kwan-gaba-kwan-baya, sai Hannatu ta yanke shawarar sake yin rajista domin yin NYSC ɗin, bisa shawarwarin da aka ba ta, a cewar wasu makusantarta da suka buƙaci a sakaya sunansu.
Sashe na 2 sakin layi na 2 na dokar NYSC ta 2004, ya bayyana cewa duk mutumin da ya kammala karatu kafin ya cika shekara 30 wajibi ne ya yi hidimar kasa, amma akan yi sassauci ga waɗanda suka yi karatun soja ko ƴan sanda ko wata ma'aikata ko hukuma ta tsaro na aƙalla wata tara, da kuma waɗanda aka bai wa girmamawa ta ƙasa.
Sai dai Hannatu Musawa da aka haifa a ranar 1 ga watan Nuwamba 1974, ta kammala digirinta na farko daga Jami'ar Buckingham da makarantar lauyoyi ta Najeriya tana ƙasa da shekara 30, don haka wajibi ne ta yi hidimar ƙasa.
Me mutane ke cewa?
Kusan sama da mako guda ke nan ana tafka zazzafar muhawara a kafafen sada zumunta na soshiyal mediya.
Akwai masu ra'ayin cewa ya kamata a bibiyi batun yayin da wasu ke ganin ba abu ne da za a tsaya ana tattaunawa a kai ba.
An ambaci sunan #HannatuMusawa da kuma maudu'in #NYSC kusan sau dubu 30 a shafin X, sannan ko Facebook da sauran kafafe idan ka leka batun ke nan da ake tafka muhawara a kai.
Kayode Ogundamisi ya ce "Idan har bayanin da ke cikin labarin @premiumtimesng gaskiya ne, to ya kamata Hannatu Musawa ta ajiye mukaminta ko kuma @OfficialBAT ya sallame ta. Ba zai yiwu a ce doka ta hau kan Kemi Adeosun ba amma ta ƙi hawa kan Hannatu.
Ya aka yi DSS ba su lura da hakan ba? Oh, hankali na kan @elrufai."
@MeLekanAdigun cewa ya yi "Abin kunya ne a ce yawancin masu ƙalubalantar Ministar raya al'adu kan batun NYSC mata ne. A iyakar sanina ba ta saɓa kowace irin doka ba, aikin minista ma hidimar ƙasa ce."
ArewaaConnect kuwa cewa ya yi "A yanzu haka Hannatu Musawa na yin NYSC, duk da cewar lamarinta ya sha banban da na Kemi.
Amma a Najeriya ne kawai wanda ya gama digiri ke buƙatar NYSC kafin ya samu aikin gwamnati amma ba ya buƙatar NYSC domin zama minista. Wannan wace irin ƙasa ce muke rayuwa a cikinta!"
Sai dai babu mamaki abin da wannan batu na NYSC ɗin Hannatu Musawa ke tunatar da mutane, shi ne badaƙalar takardar boge da ta faru a lokacin mulkin tsohon shugaba Muhammadu Buhari.
A wancan zamanin an samu tsohuwar ministar kuɗi, Kemi Adeosun da laifin gabatar da takardar yafe mata hidimar ƙasa ta boge.
An yi ta kwan-gaba kwan-baya har aka kai ga ministar ta wancan mulkin ta ajiye muƙaminta.
Sai dai labarin Hannatu ya sha bamban da Kemi Adeosun, saboda ita a yanzu ba boyayyen abu ba ne cewa tana hidimar ƙasa, sannan babu inda ta ce dama ta kammala ko kuma ta gabatar da wasu bayanai na boge a takardun da ta miƙa wa majalisa bayan tantance ta.
Me doka ta ce kan haɗa NYSC da aikin gwamnati
Wani babban lauya da BBC ta tattauna da shi, Femi Falana ya ce bisa dokokin Najeriya, duk wani mutumin da bai yi hidimar ƙasa ba, bai kamata ya riƙe muƙamin minista ba.
Domin fahimtar hakan, Falana ya ce abu na farko da ya kamata a fahimta shi ne kundin tsarin mulkin Najeriya shi ne ya wajabta yin hidimar ƙasa.
"Sashi na biyu na Hukumar kula da yi wa ƙasa hidima ta NYSC, na cewa duk mutumin da ya kammala karatu, a makarantun da ke ciki da wajen ƙasar, kuma bai kai shekaru 30 ba, dole ne ya yi hidimar ƙasa."
"Sannan sashin ya kuma ce duk wanda ya haura shekara 30 a lokacin kammala karatu an yafe masa. Don haka za a ba shi takardar NYSC da ke nuna an yafe masa".
"Sannan batun NYSC abu ne mai muhimmanci wanda doka ta tanadi duk wanda ya karya dokokinta zai fuskancin ɗaurin watanni 12 a gidan yari da biyan diyyar naira dubu 20".
Da waɗannan hujojji Falana ke cewa,"Mutumin da doka ba ta amince ya zama ɗan majalisa ba, ba zai iya zama minista ba. Saboda tsarin doka iri guda ce a kan duk wadannan muƙamai biyu.
Sashe na 147(6) na kundin tsarin Najeriya ya ƙara da cewa gwamnati ba ta da hurumin naɗa kowanne mutum minista har sai ya cancanta ya yi takarar majalisa.
Sannan sashen dokar ya ƙara da cewa duk mutumin da bai yi bautar ƙasa ba, in dai ya shaida cewa ya yi digiri to ba zai iya zama ɗan majalisa ba.
Shi ma wani masanin kundin tsarin mulki da BBC ta tattauna da shi, Mainasara Kogo na cewa in dai har Hannatu a lokacin miƙa takardunta ga majalisa ta shaida cewa ta yi digiri to wajibi ta gabatar da takardar bautar ƙasa.
Ya ce; "Sashi 174 (b) wanda ya fitar da jadawalin abin da ake buƙata kafin mutum ya zama minista, kuma batun da ya yi shi ne ya kamata mutum ya cancanci zama ɗan majalisa kafin ya zama minista".
"Takardun da ta gabatar idan ta ambato cewa a iya sakanadare ta tsaya to babu laifi, amma idan ta ce ta yi jami'a da wasu kwasa-kwasai gaba da jami'a to ya zama wajibi ta gabatar da NYSC kafin ta zama minista.
Sannan idan a takardunta akwai wanda ke nuna ba ta gama NYSC ba, to gaskiya ba ta cancanta a ba ta minista ba."
Sannan ya ce a 2020 lokacin tsohon shugaba Muhammadu Buhari an so a ba ta mukami a hukumar sanya ido kan Fansho, amma saboda ba ta kammala NYSC ba, majalisa ta bayar da shawarar a jingine ta.
Don haka idan ba ta kammala NYSC ba to gaskiya ta gurgunta tsarin dokokin Najeriya, in ji Mainsara Kogo.
Sannan masanin ya ƙara da cewa "A lokacin miƙa wa majalisa takardu, in dai har ba ka fito ka ce ka yi jami'a ko digiri ba, to ka wuce siraɗi, amma muddin ka bayyana cewa ka yi jami'a to wajibi ne ka gabatar da shaidar bautar kasa."
Ya kuma bayar da misalin wani minista cikin ministocin da aka tantance wanda bai ambaci ya yi jami'a ba, yana mai jadadda cewa ra'ayi ko zaɓin majalisa ne ta amince ta tantace shi ko akasin haka.
Mainsara ya jadadda cewa haramun ne a dokar Najeriya ka haɗa aiki biyu na bautar kasa da kuma na gwamnati.