Kwamitin amintattu (BoT) na jam’iyyar NNPP mai alamar kayan marmari sun sanar da dakatar da Rabiu Musa Kwankwaso na tsawon watanni shida saboda zarginsa da yiwa jam’iyyar zagon kasa a zaben daya gabata.
Alfijir Labarai ta rawaito Kwamitin amintattun sun fitar da sanarwar dakatarwar ta Kwankwaso a ranar Talata, 29 ga watan Agusta kamar yadda aka wallafa a shafin TVC News.
Kwamitin amintattun dai ya ce ya É—auki wannan matakin kan Kwankwaso ne saboda zarginsa da cin amanar jam’iyyar ta hanyar yiwa jam’iyyar APC aiki a zaben shekara ta 2023.
Rikici dai ya barke a jam’iyyar bayan dakatarwar da aka yiwa dan takararta na shugaban kasa kuma jagoran ta na kasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
Hakan ya biyo bayan dakatarwar da sakataren yada labaranta na kasa da wasu suka yi a baya, matakin da kwamitin amintattu ya yi watsi da shi.