A karon farko, likitocin fiÉ—a a Oxford cikin Birtaniya sun gudanar da dashen mahaifa.
Matar da aka bai wa gudunmawar mahaifar mai shekara 34 ce, yayin da wata 'yar'uwarta mai kimanin shekara 40 ta tallafa mata da gudunmawar mahaifa.
Dukkansu sun nemi a sakaya sunayensu.
Likitoci dai sun ce su biyun sun warke sarai daga aikin tiyatar da aka yi musu.
Rukunin likitoci guda 30 ne suka gudanar da aikin a watan Fabrairu, inda suka kwashe sa'a 17 suna aikin a asibitin Churchill.
Tuni dai ƙanwar tana da ƙananan yara guda biyu, kuma dukkansu 'ya da ƙanwar suna zaune ne a Ingila.
Likitan fiÉ—ar mata, Farfesa Richard Smith, wanda ya jagoranci ayarin likitocin da suka ciro mahaifar, ya shafe tsawon shekara 25 yana bincike a kan aikin dashen mahaifa.
Ya dai faÉ—a wa BBC cewa tiyatar wata "gagarumar nasara ce".