Gwamnatin Najeriya ta ce za ta fara yi wa yara mata riga-kafin cutar kansar bakin mahaifa daga ranar 25 ga watan Satumban 2023.
Gwamnatin ta ce yi wa mata masu shekaru tara zuwa 15 riga-kafin zai taimaka wajen guje wa kamuwa da cutar ta Human Papillomavirus Vaccine (HPV).
Kansa ko kuma ciwon dajin bakin mahaifa ciwo ne da ke shafar ƙwayoyin halittar wani ɓangare na mahaifa. Nau'o'in HPV kan faru ne ta hanyar saduwa kuma ita ce ta fi yawa a nau'in kansar da ke shafar mahaifa.
Rigakafin ta ka iya kare kashi 90 cikin 100 na sauran na'ukan kansar da HPV ke haifarwa.
Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce nau'ukan HPV (16 and 18), waÉ—anda ake yawan samun su a Najeriya, su ne ke haifar da kusan rabin manyan kansar bakin mahaifa a Najeriya.
An ƙiyasta cewa mata kusan 14,000 ne ke ɗauke da cutar a Najeriya, kuma mata 7,968 ne ke mutuwa sakamakon cutar duk shekara.