Cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar mai ɗauke da sa hannun babban daraktan hukumar Dakta Ifedayo Adetifa, NCDC ta ce kawo yanzu cutar ba ta ɓulla a Najeriya ba, amma hukumar na ci gaba da sanya idanu.
A ranar 7 ga watan Agusta ne aka bayyana ɓullar ƙwayar cutar EG.5 a ƙasashen duniya 51 ciki har da China da Amurka da Koriya da Japan da Canada da Australiya da Singapore da Birtaniya da Faransa da Portugal.
Hukumar Lafiya ta Duniya ta gudanar da bincike tare da gwaje-wajen kan ƙwayar cutar, inda ta gano wasu abubuwa masu yawa game da cutar.
WHO ta ce ƙwayar cutar za ta daɗe ba ta nuna wani sauyi ko alama a jikin mai ɗauke da ita ba.
EG.5 na ɗauke da alamomin da masu cutar korona ke nunawa da suka hadar da zazzaɓi mai tsanani da tari katsewar numfashi, da kasala, da ciwon gaɓoɓi, da ciwon kai da na maƙogoro.