Ƙarin ƙasashen da ƙungiyar ta gayyata sun haɗar da Saudiyya da Iran da Argentina da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da Ethiopia.
An sa rana Saudiyya mai arzikin man fetur, za ta yi tasiri sosai a ƙungiyar, musamman wajen rage ƙarfin amfani da dalar Amurka da ma ita kanta Amurkan a harkokin kasuwancin duniya.
Ƙasashen duniya 22 ne ciki har da huɗu daga Afirka suka gabatar da buƙatarsu ta shiga ƙungiyar.
A watan Janairu ne ƙasashen shida za su zama mambobin ƙungiyar na dindindin.
Batun faɗaɗa ƙungiyar ne ya mamaye kanun abubuwan da taron ai tattauna, gabanin taron da ake yi a Afirka ta Kudu.
Wasu daga cikin sharuɗa shiga ƙungiyar sun haɗar da yin biyayya ga dokokin kare hakkin bil'adama da takunkumai.
Duka shugabannin ƙasashen ƙungiyar biyar sun yi maraba da sabbin ƙasashen da suka samu zarafin shiga ƙugiyar.