Jihohin sun haÉ—a da Kebbi da Sokoto da Zamfara da Katsina da Kano da Jigawa da Bauci da Gombe da Adamawa da Yobe da kuma Borno.
Daraktan Hukumar ta NAGWW, Yusuf Maina Bukar, ya shaidawa kwamitin cewa hukumar ta kashe naira miliyan 697.71 wajen gyara ofishinta da kuma naira biliyan 11.28 wajen gudanar da manyan ayyuka.
Ya ƙara da cewa galibin kuɗaɗen da hukumar ke samu sun fito ne daga cikin kashi 15 cikin ɗari na kuɗaɗen asusun alkinta yanayi da muhalli da kuma waɗanda gwamnatin tarayya ke samarwa.
Baya ga wannan ma kwamitin ya kuma binciki Babban Bankin Najeriya game da wasu asusun ajiya fiye da bakwai da bankin ya san da su.
Wasu takardun bayanai masu shafuka shida ɗauke da kwanan watan 22 ga watan Agustan 2023 da bankin na CBN ya miƙawa kwamitin sun nuna cewa an sakawa asusun hukumar kimanin naira 9,465,960,382.57 tun daga 2015 zuwa wannan ranar.
Babban akanta janar na Najeriya, Oluwatoyin Madein ya bayyana cewa Hukumar da ke lura da shirin dashen itatuwa da alkinta yanayi ta NAGWW ɗin ta ƙarbi kuɗin da yawan sa ya kai naira 19,377,726,506.95 tun daga watan Febrairun 2019 kawo yanzu.
Shugaban kwamitin binciken na majalisar wakilai ta Æ™asa, Isma’ila Haruna Dabo tare da sauran mambobin kwamitin sun nuna damuwa yadda aka kashe kuÉ—in babu kan gado.
Kwamitin ya bayyana cewa ya zama wajibi su gudanar da cikakken bincike kan wannan batu duba da irin maƙudan kuɗaɗe da hukumar ke samu daga gwamnatin tarayyar Najeriya da ma sauran ƙasashen waje amma ta sauka daga kan turbar da aka ɗora ta a kai.