Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya miƙa ta'aziyarsa da gwamnati da al'ummar Afirka ta Kudu kan mummunar gobarar da ta yi sanadiyyar mutuwar mutune da dama a birnin Johannesburg.
Cikin wani saƙo da mai magana da yawun shugaban ƙasar, Ajuri Ngelale ya sanya wa hannu, Tinubu ya ce yana miƙa ta'aziya da alhinisa ga iyalan mutanen da suka mutu, sakamakon gobarar.
"A wannan mawuyacin lokacin na alhini, al'ummar Najeriya na jajanta muku kan wannan mummunan abu da ya faru".
Tinubu ya kuma yi addu'ar samun sauƙi ga mutanen da suka samu raunuka sakamakon gobarar.
Kimanin mutum 73 ne aka bayyana cewa sun mutu, yayin da 43 suka samu munanan raunuka sakamakon gobarar da tatashi a ƙasar ta Afirka ta Kudu.
Wasu rahotanni na cewa galibin mutanen da ke cikin ginin da gobarar ta rutsa da su baƙin haure ne, da kuma ke zaune a ginin ba bisa ƙa'ida ba.