Kwamitin zaman lafiyan ya buƙaci kowane bangare na jam'iyyun dake jiran sakamakon zabe daga kotun saurarar ƙararrakin zabe ta jihar kano da kada suyi amfani da rashin jin daɗin sakamakon su tada hankalin al'ummar jihar kano. Kwamitin dake samun jagoranci ƙarƙashin shugabancin Most Rev. Dr. John Namaza Niyiring, Kano Bishop na Kano da Jigawa, da kuma daya shugabancin na riko karkashin jagorancin A. B. Mahmoud (SAN). ya nemi al'ummar jihar kano masu son zaman lafiya dasu dunƙule guri ɗaya domin a cigaba da samun ingantaccen zaman lafiya kamar yadda yake.
Yayin tattaunawa da ƴan jaridu Shugaban sakatariyar kwamitin zaman lafiyar na jihar Kano Amb. Ibrahim Waiya, ya bayyana yadda sukayi iya ƙoƙarin su na ganin Kano ta zauna lafiya kafin ayi zabe dama bayan zabe wanda ba don komai suka samu wannan nasara ba sai don haɗin kai da manyan jam'iyu musam man manyan bangarori biyu na NNPP da kuma na APC, suka basu na ganin ba'a samu wani matsala da zai kawo hargitsi ko makamancin sa a yayin gudanar da zabe da kuma bayan zabe na shekara ta 2023
A ƙarshe Amb. Ibrahim Waiya yace zasu cigaba da tuntubar jagororin jam'iyyun bangarorin domin tabbatar da an samu zaman lafiya a jihar Kano, a kowa ne lokaci.
Daga karshe Amb. Ibrahim Waiya, Yayi fatan dorewar samun zaman lafiya a Jihar Kano, da Nigeria baki daya.