Kotun ta kuma soki da'awar lauyoyin Uba Sani na cewa masu ƙorafi sun shigar da ƙara, bayan lokaci ya wuce, don haka ta yi watsi da buƙatar da suka nema.
Alƙalan kotun sun yanke hukuncin ne ranar Alhamis ta hanyar Zoom.
Wakilan ɓangarorin biyu da lauyoyinsu sun halarci zaman kotun a Kaduna, sai dai alƙalan wadanda ba su hallara a kotun ba, sun karanta hukuncin ta majigi.
Isah Ashiru na jam’iyyar PDP ne ya shigar da Æ™arar, inda ya yi zargin tafka maguÉ—i a zaÉ“ensu na watan Maris.
Sakamakon da hukumar zaÉ“e mai zaman kanta ta Najeriya, ta fitar a watan Maris, ya nuna cewa Sanata Uba Sani na APC, ya samu Æ™uri’a 730,002.
Yayin da Isa Ashiru na PDP ya tashi da Æ™uri’a 719,194.