Monu Manesar, wanda ke jagorantar masu tsattsauran ra'ayin Hindu, na cikin waɗanda suka assasa shirin kare shanu, waɗanda ke da martaba a addinin Hindu.
Ana zargin shi da haddasa rikici a lardin Nuh.
Haka nan ana zargin shi da jagorantar wani mummunan duka da aka lakaɗa wa wasu matasa musulmai a yankin Rajasthan.
Bayanai sun ce ya wallafa wasu bayanai na tayar da husuma a shafukan sada zumunta gabanin tattakin na mabiya addinin Hindu da aka yi a Haryana, wanda ya janyo tashin hankali.