Rundunar ƴan sanda a Najeriya ta ce ta tsaurara tsaro a faɗin ƙasar domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiya gabanin yanke hukunci kan ƙarar da aka shigar kan zaɓen shugaban ƙasar.
A cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar ta hannun jami'in hulɗa da jama'a na rundunar na ƙasa, ACP Olumuyiwa Adejobi, ta ce, rundunar ta baza jami'anta a kowane ɓangare na faɗin ƙasar gabanin sanar da hukuncin kotun a ranar Laraba.
A ranar Litinin ne dai kotun ta sanar da cewa za ta yanke hukunci kan ƙorafe-ƙorafen da aka shigar a gabanta game da babban zaɓen na Najeriya a gobe Laraba.
Manyan jam'iyyun hamayya na ƙasar, PDP da LP, da ƴan tsakararsu na shugaban ƙasa ne suka shigar da ƙara suna ƙalubalantar nasarar da Bola Ahmed Tinubu na jam'iyyar APC ya samu a zaɓen da aka gudanar cikin watan Fabarairun shekara ta 2023.
Sanarwar da rundunar ƴan sandar ta fitar ta kuma ja kunnen waɗanda ta kira masu 'mummunan fata' da ƴan siyasa, da su guji yaɗa bayanai na ƙarya, kasancewar rundunar ba za ta lamunci duk wani yunƙuri na tayar da husuma ko hargitsi tsakanin al'umma ba.
"Rundunar ƴansanda ta tura jami'anta tare da ɗaukan duk matakan da suka kamata a wannan lokaci, kuma jami'anta a shirye suka su tabbatar da doka.' A cewar sanarwar.