Wannan na ƙumshe ne a wani bayani da ya fito ta hannun Sakataren hukumar Adam Bababe, wanda ya ce an lura da yadda ake ci gaba da samun yawaitar mutanen da ke bayar da hayar filayensu da ke a wuraren da ake kasuwanci inda ake amfani da su a matsayin gidajen caca.
Sanarwar ta ce, "Hukumar ta BOGIS na sanar da al'umma cewa ta lura da yadda ake bayar da filaye barkatai ko dai saboda kasuwanci ko ginin gida ko kuma masu gudanar da ayyukan caca su yi amfani da su, kuma hakan ya saɓa ma doka".
"Samun waɗannan wuraren sharholiyar da ake yin caca a jiharmu ya haifar da ƙorafe-ƙorafe daga jama'a kasancewa ana samun matasammu da dama da ke shiga munanan ayyuka inda suke neman kuɗin da za su yi cacar". "A kan haka, hukumur tara bayanan filaye BOGIS na nanata cewa samar da irin waɗannan wurare da suka shafi shagunan da za a yi amfani da su wajen gudanar da caca ya ci karo da doka", in ji Bababe.
Ya bayyana sashe na 13 ƙaramin sashen na 2 na dokar kula da filaye ta jihar Borno ta shekarar 2022, ta tilasta wa masu wurare da su martaba ƙa'idojin da aka gindaya musu na mallakar wuri