Iyayen na wannan koke ne yayin da aka buɗe makarantun boko a duk fadin ƙasar bayan dogon hutu, domin fara sabuwar shekarar karatu.
Yawancin iyaye da mariƙan na cewa wannan yanayi ya jefa su cikin hali na tababa game da cigaban karatun 'ya'yan nasu ganin cewa kuɗaɗen da suke samu ba su ƙaru ba yayin da ɗawainiya ta tsadar rayuwa ta ƙaru sosai.
Ƙarin kuɗin ya zo ne a wani lokaci da aka sami koma-baya game da kuɗin da iyalai ke samu, musamman saboda fadi tashin hauhawar farashin kayayyaki da ayyuka, wanda cire tallafin man fetur ya haddasa.
A irin wannan lokaci na komawa makaranta yawancin yara na kasancewa cikin murna da shauƙi na komawa makaranta.
Sai dai kuma komawar a wannan karon ta zo wa iyaye da damuwa, sakamakon ƙarin kuɗin makarantun da yawancin makarantu masu zaman-kansu suka yi a duk faɗin ƙasar.
Matsin tattalin arziki da tsauwalar rayuwa da cire tallafin man fetur ya haifar ne suka tilasta ƙarin kuɗin na makaranta, a cewar jami'ar wata makarantar kuɗi da ke Abuja, babban birnin tarayyar Najeriyar:
''Kowa dai ya san matsalar ya zama ruwan dare ya shafi kowa da kowa shi ya sa muka yi ƙarin kuɗin makaranta.''
Jami'ar ta ƙara bayani da cewa, '' ka ga za a biya malamai ga haraje-haraje da ake biya ga kuɗin sayen takardu, abin rubutu ga su nan dai kuɗin wuta kuɗin ruwa da sauransu.''
Ta ce, su ma ba da sonsu suke ƙara kuɗin ba domin idan ba su yi hakan ba ta yaya za su iya biyan malamai, har a samu yaran su yi karatu?