Gwamnatin jihar Benue ta tabbatar da sace kwamishinan yaɗa labarai da al’adu da yawon shaƙatawa, Matthew Abo da kuma tsohon shugaban karamar hukumar Ukum, Iorwashima Erukaa.
Babban Sakataren yaɗa labarai na gwamnan jihar, Tersoo Kula, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, ya ce wasu ‘yan bindiga ne suka yi garkuwa da Abo a gidansa da ke Sankara da misalin karfe takwas ranar Lahadi da daddare, yayin da aka yi garkuwa da Erukaa a ranar Asabar.
“Ƴan bingidan da suka yi garkuwa da mutanen biyun da har yanzu ba a san inda suke ba, sun tuntubi iyalan Erukaa amma har yanzu ba su tuntubi dangin Abo ba,” in ji sanarwar.
"Gwamnan wanda ya bayyana lamarin a matsayin abin Allah-wadai kuma abin da ba za a amince da shi ba, tuni ya umarci hukumomin tsaro da su fara aiki nan take domin ganin an sako mutanen biyu cikin koshin lafiya."
Gwamnan ya kuma yi kira ga al’ummar jihar da su kwantar da hankalinsu, domin gwamnatinsa za ta yi duk mai yiwuwa domin ganin jihar ta kasance mai aminci ga kowa.