A kwanakin nan dai ana ta fama da cece kuce kan batun shugabancin ƙungiyar wanda wasu tsirari ke iƙirarin kawar da shugabancin tare da kira da babbar murya wajen ganin cewa anyi zabe kamar yadda suke faɗe.
Ana tsaka da wannan dambarwa ne akaji wasu daga cikin ƴan ƙungiyar har ma da waɗanda ba halastattun ƴan ƙungiyar ba sun tara taron manema labarai suna faɗin sun rushe shugabancin KCSF kuma sun wakilta kansu matsayin shugabancin ruƙo a madadin mambobi wannan ƙungiya.
Kwamitin Amintattun sunyi kira da a ɗauki wancan zance a matsayin zancen ƙanzon kurege kuma zancen da bashi da tushe balle makama.