Inda yasamu damar karbar belin matasan da azal ta fada musu, wanda har takaisu da tsare su a gidan ajiya da gyaran hali. Da suke bayyana farincikin su sun bayyanawa wakilinmu Jamilu Lawan Yakasai cewar tabbas basu tunanin haka ba.
Sakamakon su 'yan talakawa ne wanda iyayensu hakan yasa suka fidda ran fita a wannan lokaci, sai dai babu zato babu tsammani sai ga Dan Majalissar su ya kobutar dasu.
Inda sukai mishi godiya da fatan alkhairi.
Shima anasa bangaren yace wadannan matasa da azal ta fada musu kannansa ne kuma yan uwansa ne, a don haka yayi musu addu'ar Allah ya kiyaye gaba.