Madatsun ruwan sun fashe a Derna bayan gawurtacciyar guguwar Daniel ta auka wa Libya a farkon wannan mako, inda ya malalo ruwan saman da ba a taɓa gani a wasu yankunan gaɓar tekun ƙasar.
Guguwar ta taho da ruwan sama kamar da bakin ƙwarya fiye da tsayin inci 16 kwatankwacin milimita 400 a yankunan gaɓar tekun cikin sa'a 24.
Ruwa ne mai yawan da ba a saba gani ba a yankin da galibi abin da ake samu bai fi milimita 1.5 ba kawai a ɗaukacin watan Satumba.
Ko, kuma dai kawai a ce fiye da ninki 260 na ruwan saman da akasari yake sauka cikin wata ɗaya, amma wannan karo a cikin kwana guda.
Bayanai daga tauraron ɗan'adam sun nuna yawan ruwan saman da aka yi a faɗin yankin - ko da yake a wasu wuraren ruwan da ya sauka ya fi yawa.
Ɓarna mafi muni da aka gani ta faru ne, sanadin bala'in ambaliyar ruwa bayan fashewar madatsun ruwa biyu a kan Kogin Wadi Derna.
Kogin Derna dai, akasari bai fiye cikowa ba, amma ruwan sama a wasu 'yan lokuta yakan tumbatsa a madatsun.
Madatsun biyu suna tare ruwa mai yawan da ya kai nauyin tan miliyan ɗaya da rabi, sannan haɗuwar ƙarfin ruwan da ke kwarara da tarkacen da ya riƙa cin karo da su ne, ta ƙara munin ɓarnar da aka samu.
Shaidu sun ce ruwan ya kai kusan mita uku wato ƙafa goma a wasu wurare.
Gudun ambaliyar ruwan da ya kai tsawon inci shida, ya isa ya tunkuɗe mutum ƙasa, haka zalika ruwa mai tsawon ƙafa biyu kawai yana iya ɗaga mota ya tafi da ita.
Mutane fiye da 20,000 ake fargabar sun mutu
Sama da mutum 20,000 ne ake fargabar cewa sun mutu a ambaliyar ruwan Libya, a cewar wani jami'in gwamnatin yanki.
Bala'in ambaliyar ruwan ya shafe gabashin ƙasar ranar Lahadi.
Magajin birnin Derna na gaɓar teku ya faɗa wa tashar talbijin ta Saudiyya mai suna Al Arabiya cewa ya yi ƙiyasi kimanin mutum 18,000 zuwa 20,000 ne suka mutu lokacin da madatsun ruwan birnin suka fashe, inda ambaliyar ruwan tsunami ta yi awon gaba da mutane a lokacin da suke gida suna barci.
Alƙaluman da ya bayar sun dogara ne a kan adadin unwagunnin da ambaliyar ta ɗaiɗaita, kamar yadda ya faɗa wa gidan talbijin ɗin.
Gawawwakin da ba a kai ga ganowa ba har yanzu na ƙarƙashin ɓaraguzai ko kuma can a cikin teku, lamarin da ke ƙara kasadar ɓarkewar cutuka.
Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce gwamnatoci biyu da ke gaba da juna a Libya suna aiki tare, wajen tsara aikin taimakon mutanen da mummunar ambaliyar ruwa ta faɗa wa a kwana huɗu da ya gabata.
Hukumomin biyu, da wadda ke mulkin yammacin ƙasar da kuma mai mulki a gabashi inda bala'in ya auku sakamakon mahaukaciyar guguwa mai tafe da ruwan sama da aka yi wa laƙabin Daniel, suna ta kira ga hukumomi da ƙasashen duniya su agaza.
Ana ta samun ƙaruwar waɗanda suka mutu, bayan sama da dubu biyar da aka tabbatar zuwa yanzu.
Jami'ai na ganin yawan waɗanda bala'in ya hallaka zai iya kaiwa kusan dubu uku.
A ranar Lahadi wannan bala'i na ambaliya da ke kama da Tsunami, ya afka wa ƙasar ta Libya a ɓangaren gabashi.
Ambaliyar ta haddasa ɓallewar madatsun ruwa da gadoji a birnin Derna inda lamarin ya fi ta'adi.
Hukumomin ƙasar biyu da ba sa ga maciji da juna, a yanzu sun kawar da wannan gaba, inda suka zamanto kamar ciki ɗaya wajen tsara aikin agaji.
Gwamnatin da ke iko da yammacin Libya wadda Majalisar Ɗinkin Duniya ta amince da ita, na dafa wa abokiyar gabar tata da ke gabashi, inda bala'in ya afku.
Hukumomin biyu na ta kira ga ƙasashen duniya da su taimaka, yayin da teku ke ta angizo tarin gawarwakin mutanen da ambaliyar ta hallaka.
Masu aikin agaji na ta faman suturta su, bayan iyalai da 'yan uwa sun gane nasu, ana kuma binne su a manyan ƙaburbura na bai-ɗaya.
Kusan a ko da yaushe ƙaruwar alƙaluman waɗanda suka rasu ake yi, da bayyana ko gano wasu ƙarin gawarwaki, bayan sama da dubu biyar da ɗari uku da aka samu a birnin Derna.
Tauhid Pasha na hukumar da ke kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya ya yi wa BBC bayani kan yadda gwamnatocin biyu na ƙasar ke aiki tare:
Ya ce, abin mamaki ne a ce, gwamnatocin biyu na kira ga hukumomin duniya suna neman taimako.
Ƙalubalen yanzu shi ne ƙasashen duniya su amsa yadda ya kamata ga buƙatu da kiran na gwamnatocin.’’