BUDADDIYAR WASIKA ZUWA GA MAI GIRMA SHUGABAN KASA SANATA BOLA AHMED TINUBU GCFR, DAGA MAJALISAR MATASAN AREWA (MAJALISAR MATASAN AREWA)
Yallabai,
MUNA KIRA DA KADA KAYI AMFANI DA ƘARFIN IKON GWAMNATI KAMAR YADDA AKE ZARGI WAJEN SHIGO DA SIYASA A JIHAR KANO DOMIN ILLA CE GA SIYASAR KA KUMA ZAI GOGE DUK WATA SOYAYYA DA AKE MAKA SANNAN YA KAWO CIKAS GA DIMOKARAƊƊIYYA A JIHAR.
Mu dai kamar yadda muka ga ya dace mu gabatar maka da kungiyarmu, kasancewar wannan shine karo na farko da muka rubuto maka wasika tun bayan daka ɗare kujerar mulki a matsayin zababben shugaban kasar Tarayyar Najeriya. (Majalisar Matasan Arewa), kungiya ce mai mayar da hankali ga matasa zalla, wacce aka kafa a shekarar 2010, sannan aka mata rijista da CAC. Kungiyar tana aiki da duba tsarin shugabancin kasa da na Jihohi goma sha tara na Arewa ciki har da babban birnin tarayya Abuja.
Ranka ya dade mun kuduri aniyar tattaunawa da kai ta wannan kafar, domin kaucewa ka’idojin da ba su dace ba, da tsarin gudanar da mulki, la’akari da girman al’amarin, da kuma gaggawar jawo hankalinka a kan lamarin, kafin al'umma su fita daga hayyacin su.
Kamar yadda ka sani, Kano a hukumance ita ce jiha mafi yawan al’umma a fadin najeriya, inda akai kiyasin sama da miliyan 20, shine yawan al’ummar dake cikin ta, wanda yawan su ya kai yawan al'ummar jihohi 5 idan aka hada su a kasar nan. Jihar Kano, ita ce cibiyar kasuwanci kuma zuciyar Arewa, wadda yawancin al’ummar wasu jihohi sun dogara ne da ita, wanda hakan ke samar da cigaban tattalin arzikinsu, da kuma cigaba da samun abin dogaro da kai.
Jihar kano ta ɗau seti a siyasance tun daga shekarar 2019 bisa taimako da agaji da wasu ƙungiyoyi ke baiwa jihar don samar mata da yanayi mai kyau irin su kwamitin zaman lafiya wato Kano Peace Committee (KPC) wanda a lokacin CP Muhammda Wakili ya tattaro kan mu y zauna damu domin fito da wasu hanyoyi wanda za abi a samarwa da jihar kano zaman lafiya amma duk da wannan ƙoƙari sai da wasu marasa kishin jihar kano suka ƙiƙiro mana da inconclusive ba don waɗannan ƙungiyoyi ba da anyi asarar rayuka a jihar.
Zaben 2023, ya gudana daidai gwargwado cikin lumana, sakamakon hadin gwiwar hukumomin tsaro, kwamitin zaman lafiya na Kano (KPC), da kuma hadin kan gwamnatin jihar Kano. Jihar Kano ta samu kubuta da dama daga cikin rashin tsaro da ake zargin an tsara su ne domin jawo jihar cikin rudani da rashin jituwa. Dukkanmu muna sane da yanayin jama'a mabanbanta ƙabilu a Jihar tare da bambancin addini, al'adu da tsarin zamantakewa.
Yallabai,
rashin adalci na tsarin, shari'a dana hukumomi a nahiyar afirka, sun bayyana dalilin daya sa tsarin dimokaraɗiyya ke cigaba da ingiza al'ummar ƙasashe cikin ruɗani da fushi domin sun rasa kwarin gwiwar da tsarin ya basu, kuma hakan na iya fitowa a fili ta hanyar nuna rashin adalci a zaben da al'umma ke yi amma kuma a basu wanda basu zaba ba, wani lokacin ma kwace musu zaben ake yi bayan hukumar zabe ta sanar da wanda suka zaba, duka ta hanyar zabe ko ƙarfin iko a hukumomin shari'a. Wannan wani mugun aiki ne da wasu ‘yan siyasa masu son zuciya da mugayen tunani suke yawan shiryawa ƴan ƙasa, wadanda basu damu da makomar kasar nan ba, sai dai kawai don biyan bukatarsu ta siyasa, duk da cewa a lokacin zabe ne. illa ga yawan masu zaɓe. Wannan Ra'ayinmu ne cewa, idan har tsarin dimokuradiyyar Najeriya ya cigaba da tafiya bisa rashin adalcin zabe da gurgunta kyawawan ayyukan gudanar da mulkin dimokuradiyya, bisa adalci ga dukkan bangarorin, to lallai abin da zai biyo baya zai yi barnar da babu mai iya shawo kanta sai Allah.
Ranka ya dade, mu ’yan kasa ne masu bin doka da oda, kuma mun yi imani da bin doka da oda, duk da haka, ba wai kawai yin adalci a rubuce ko a baki ba, amma a fili aga anyi. A bar Bangaren shari’a a matsayin bangaren Gwamnati mai cin gashin kansa, ana sa ran zai zama hanya ta karshe ga talaka wanda zai ya zuwa ya nemi haƙƙin sa, duk da haka, indai ƴan kasar nan suka fara nuna shakku kan rashin adalci na bangaren shari’a a cikin tsarin shari’a, to tabbas kasar nan wataran za'a wayi gari cikin tashin hankali mai tsanani.
Mun samu abin takaici, bayanai da ke zargin cewa akwai sa hannun wasu a cikin Gwamnatin ka cewa sun yi katsalandan tare da yin magudi a kan hukuncin kotun sauraron kararrakin zaben Gwamnan Jihar Kano, labarin da idan har ya zama gaskiya, to tabbas za a iya bayyana shi a matsayin abin takaici, wanda ba a taba ganin irinsa ba, kuma muma muna Allah wadai da wannan abu. Jihar Kano, a halin da ake ciki, irin wadannan ikin tir na rashin jin dadi na iya haifar da rikicin siyasa a jihar, kuma zai iya haifar da yanayin da sai gwamnati ta ƙwammace kiɗa da karatu.
Kano ana daukarta a matsayin cibiyar kasuwanci ta jijiyoyi ba kawai ga Arewa ba, har ma ga daukacin kasashen da ke kudu da hamadar Sahara, wadanda ke da alaka daya da jihar Kano. Jihar Kano dai za'a iya kwatanta ta a matsayin abin koyi, kuma a matsayin yanki mafi dabarun siyasa da ilimi da wayewar siyasa da kyakykyawan zaman lafiya. Amma Bisa la’akari da haka, Kano tana da rauni kuma idan aka kakkarya ta, tabbas kai tsaye barazana ne ga tsaron kasa.
Yallabai,
bari mu tunawa tuna maka, tun daga 1999 zuwa 2007, lokacin da kayi Gwamnan Jihar Legas, a lokacin AD. Jam’iyyarku ta sha bamban da jam’iyyu a najeriya, kuma duk da rashin fahimtar juna da aka yi, mai girma Olusegun Obasanjo ya jagoranci gwamnatin tarayya bai yi wani yunkuri na kwace wa’adin da mutanen jihar Legas nagari suka baku ba domin da yaso zai iya ƙwace kujerar ka duk da cewa zabar ka akayi don tafiyar da al’amuran jihar bisa doron doka da oda kuma sai da ka gama daga 1999 zuwa 2007. Don haka barin wasu da ake zargin ‘ya’yan Gwamnatinka ne, su shirya makarkashiyar kwacewa al’ummar Kano gwamnatin su ba dai-dai bane, wannan ƙiyayya ce ƙarara ga al'ummar jihar kano, kuma an fara samun shakku kan kudurorinku na tabbatar da tsarin dimokuradiyya, da aka kafa a tsarin zabe. Wannan rashin adalci yasa ƴan najeriya sun dena jin akwai adalci a gwamnatin ku.
Makircin da ake ganin wasu da ake zargin suna cikin Gwamnati ne, wanda ba don komai suke shirya hakan ba sai domin ruguza Jihar Kano, sakamakon idan rikici ya fara a kano ba lallai ya kare ba, kuma ko shakka babu abin zai haifar da mummunar illa ga sauran jihohin tarayyar najeriya. Don haka amfani da siyasa wajen tayar da rikici a Kano, ta hanyar kotun sauraren kararrakin zaben gwamna, tabbas misali ne na haifar da rikici wanda zaiyi wuya a shawo kansa, bisa ga tada zaune tsaye, sakamakon hukuncin kotun sauraron kararrakin zaben Gwamnan Jihar Kano. Don haka babu wani lokaci daya fi dacewa da kuyi aiki da rashin adalci, kamar yanzu don daƙile afkuwar lamarin, ta hanyar yin galaba akan ‘yan jam’iyyarku da ake zargin suna da hannu a cikin wannan rikon sakainar kashi na siyasa.
Sa hannu:
Dr. Ali Idris
Mukaddashin shugaba na kasa
Sakataren Yada Labarai na Kasa.
Comrade Adikwu Omale Joshua