Al'ummar wannan yankin sun matukar nuna jindadin su na wannan cigaba da harkar ilimi yasamu a yankin su.
Wasu iyaye sun shaida cewar sun shafe shekaru Takwas "8" suna kira ga mahukunta kan sukawo wa yaran su dauki, amma mahukunta sukai funfurs da rokonsu.
Da yake shaidawa wakilinmu Jamilu Lawan Yakasai Hon Dr Zakariyya Al-Hassan ya bayyana masa cewar " Burunsa ace yankunan da yake wakilta sun zama sunbukasa fiye da kowanne bangare a Jihar Kano, Inda yakara da cewar a yanzu haka akwai wasu aikace-aikace na cigaba da yankin Kura/Garun Malam zasu kara samu.
Inda yakuma kira da al'ummar Kano wajen bawa Gwamnatin Kano goyon baya domin cigaba da kurbar roman dimukradiyya.