Dr Zakariyya ya kansance wanda yakewa jagorantar al'ummar kura da garun malam a karkashin inuwar jam'iyyar NNPP ta Engr Rabi'u Musa Kwankwaso, yace duk manufufin tsohon gwamnan Kano jagoransu a siyasance dasu yake koyi.
Inda yace babban burinsa shine yaga ya sauke duk wasu alkawarurruka dayayi wa al'umma a yayin neman kuru'un al'ummar dayake wakilta, dama alkawarurrukan da bayyi musu ba.