Hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta ce ta kama wani da ake zargi da karkatar da kayan tallafi a jihar Nasarawa.
DSS ɗin ta ce ta samu nasarar kama mutumin ne bayan samun rahotanni daga wasu gwamnatocin jihohi da ke cewa ana karkatarwa ko kuma sayar da kayan tallafin.
Cikin wata sanarwa da hukumar ta DSS ta fitar, ta ce a binciken da tayi, ta samu nasarar gano wasu daga cikin kayan abincin da kuma gurfanar da waɗanda ake zargi.
DSS ta ce ta kama wani mutumi a jihar Nasarawa wanda ake zargi da karkatar da kayan tallafin da aka yi niyyar raba wa masu karamin karfi.
Cikin waɗanda aka kaman, har da jami'an hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar Nasarawan (NASEMA) da abokan aikata laifin a kasuwanni.
Yanzu an miƙa mutanen zuwa hannun hukumomi domin ɗaukar mataki a kansu.