GWAMNATIN KANO TA CANCANCI YABO NA MUSAMMAN DUBA DA YADDA TA ZABTARE KASO 50% NA KUƊIN KARATU NA ƊALIBAI 7000 DA TAYI.
Cibiyar Bunƙasa Cigaban Ƴan Kasa (CDE) tana fatan yabawa Mai Girma Gwamnan Jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf bisa tallafin da ake bai wa ’yan asalin Jihar Kano da ke karatu a Jihar Kano. Mallakar manyan makarantun gwamnati, ta hanyar rage kashi 50% na kudaden makaranta. a matsayin tallafin ilimi da Gwamnan Jihar yayi a dai-dai lokacin daya dace. Musamman idan aka yi la'akari da halin da tattalin arzikin Najeriya ke ciki a halin yanzu na mawuyacin hali.
Mun ga cewa ya zama wajibi mu yabawa Eng. Abba Kabir Yusuf, bisa bayar da wannan tallafi ga iyaye da daliban da ke karatu a manyan makarantun mallakar gwamnati, wanda abu ne mai wuya su samu kudin shiga makarantar a dai-dai wannan lokaci.
Hakazalika, shiga tsakani na daidaita kudaden karatun dalibai sama da 7000 na jihar Kano, dake karatu a jami’ar Bayero. Wannan taimako na musamman ya ceci dimbin daliban jihar Kano, wadanda tuni suka yanke shawarar daina karatunsu.
Don haka, wannan aikin ya cancanci yabo, domin an ceci makomar ɗalibai da yawa daga halaka.
Daga karshe muna kira ga mai girma gwamnan jihar Kano da ya mikawa sauran daliban jihar Kano da suke karatu a wajen jihar makamancin wannan tallafi.
Fatan CDE shine, sauran Gwamnonin Jihohi za suyi koyi da wannan hangen nesa.
Sa hannu
Daraktan Zartarwa na
Cibiyar Bunƙasa Cigaban al'umma
CDE
Amb. Ibrahim Waiya