Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya bayar da umarnin dakatar da shugaban kamfanin samar da kayan aikin gona na jihar (KASCO), bisa zargin shi da sayar da hatsi mallakar gwamnati.
Sanarwar da babban sakataren yaÉ—a labarai ga gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar, na cewa a ranar Talata 12 ga watan Satumban 2023 ne, Gwamna Abba Kabir, ya bayar da wannan umarni.
Sanarwar ta ce ana zargin Dr. Tukur ÆŠayyabu Minjibir, ne da sayar da hatsin gwamnati, ba ta hanyar da ta dace ba.
Gwamnatin jihar ta umarci Dr Tukur Ɗayyabu, ya miƙa ragamar gudanar da kamfanin ga jami'i mafi girman muƙami nan take, ya zuwa lokacin da za a ji sakamakon ƙarin bincike.