Gwamnan Jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf Ya Kaddamar Da Rabon Abinci ga Talakawan Jihar Karkashin Hukumar Raya Karkara da Bunkasa Noma KNARDA.
Alhaji Abba Kabir Yusif ya jagoranci Raba Kayan Masarufi Da Suka Hadar Da Dawa, Masara, Shinkafa, da sauransu, yayinda a bangaren Dabbobi Kuma aka ba da Awaki Da Tinkiya Da Raguna.
Sai Kuma kayayyakin Noma da suka Hada da Injinan Barza Dana Nika Dama Injin Ban Ruwa Na Zamani Mara Amfani Da Manfetir Da Takin Zamani Da Iri.
An rawaito mana cewar, Gwamnan ya Kaddamar Da Samfurin Kayan ne da za’a Rabasu A Dukanin Kananan Hukumomi Arba’in Da Hudu Dake Fadin Jihar Kano, haka Kuma gwamnan yace kimanin gidaje dubu biyar ne zasu samu Tallafin.